Ciniki na tsarin biya da kadan- kadan
Tambaya
Hukuncin siyan mota ta hanyar biyan kudi kadan-kadan
Amsa
Abin da aka tsara shi ne halascin cinikayya bisa tsarin biya kadan- kadan tare da kara kudin kayan sayarwan, amma da sharadin biyan kudin kadan-kadan ya zama an san lokacin biya, kuma an san jimillar kudin da adadinsa.
Kuma babu laifi irin wannan mu’amalar ta gudana karkashin kulawar banki, (a matsayin mai bayar da kudin saye), irin wannan tsarin na ciniki ba ya cikin irin bashin da ake samu na amfani da hanyar riba wanda aka haramta, idan mutum ya sayi mota a tsarin biyan kudi kadan-kadan ta hanyar banki tare da karin farashi wurin biya, to wannan abu ne da ya halasta a shari’ance da babu wata matsala a ciki.