Mikewa yayin wucewa da gawa

Egypt's Dar Al-Ifta

Mikewa yayin wucewa da gawa

Tambaya

Mene ne hukuncin mikewa yayin wucewa da gawa?

Amsa

Akanso wanda yaga jana’iza zata gilma ta gabansa ya mike har sai ta wuce, shi kuma mai raka gawar ya cigaba da kasance a yanayi na tsayuwa har sai an sanya gawar a kabari.

Yazo a cikin Sunnah maigirma umurnin mikewa jana’iza, Annabi SallallaHu AlaiHi Wasallam ya ce: (Idan kuka ga jana’iza to ku mike mata, wanda ya rakata kuma to kada ya zauna har sai an sanyata a cikin makwanci) Bukhari.

Hakanan daga Jabeer bin Abdallah Allah ya kara musu yarda yana cewa: Anzo wucewa da wata gawa, sai Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam ya mike, sai muma muka mike, sai muka ya ce:  Ma’aikin Allah, gawar fa ta bayahude ce! Sai Manzon Allah ya ce: (Lallai ita mutuwa abace mai razanarwa, to idan kuka ga gawa ku mike mata) Muslim.

A cikin wadannan hadisan da sukayi umurni da mikewa janaza har sai ta wuce ko har sai an sanyata a kabari, kuma da umurtan wanda yake mata rakiya da kada ya  zauna har sai bayan an sanyata a kabari, shin gawar ta musulmi ce ko na wanda ba musulmi, shi ne ma’anar fadin Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam: (Shin gawa ba mutum bace?) to wannan shi ake bukatar yiwa kowace janaza.  

Share this:

Related Fatwas