Marhalan karewar kulawa da maraya.

Egypt's Dar Al-Ifta

Marhalan karewar kulawa da maraya.

Tambaya

Wace shekara ce ko matakin rayuwa da idan maraya ya kai za a dena kulawa da shi?

Amsa

Shi kulawa da maraya yana daga cikin manyan ayyuka masu girma, saboda a cikin kulawa da maraya akwai sauke  nauyi ga raunin marayan, kuma hakan yana zama madadi ne na iyayen da shi marayan ya rasa, saidai raunin maraya yana tashi ne a lokacin da shi marayan ya samu karfi na wadatuwa da waninsa tare da ikon jan ragamar kansa da kansa, wannan yana nuna cewa kula da maraya baya tashi saboda ya balaga, yana cigaba ne har sai lokacin da shi marayan ya wadatu daga duk wani agajin waninsa, da iya gudanar da lamuransa da kansa, kuma kulawa da maraya na wanzuwa har zuwa lokacin da aka rasa abin bukata, kuma ladan kulawar na cigaba har zuwa lokacin bukata, lura da wannan lamarin da iyakanceshi yana sabawa ne bisa la’akari da lokaci ko wuri da kuma yanayi, abin nufi dai anan shine tabbatar da manufar bayar da kulawa koda kuwa hanyoyin tabbatar da hakan sun banbanta.

Share this:

Related Fatwas