Ziyaran kaburburan waliyai da salih...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ziyaran kaburburan waliyai da salihai.

Tambaya

Shin ya halasta a niki gari zuwa kaburburan salihan bayi domin ziyara?

Amsa

Ziyartan kaburbura lamari ne da aka shar’anta, a bisa yanayi na yalwa, wanda ya halasta ga maza da mata, duk wani abu da ya zama abin shar’antawa a bai daya to ana sanya shi cikin mustahabbi musamman idan ya rataya da Annabawa ko salihai daga cikin al’ummar Annabi SallallaHu AlaiHi Wassalam, kamar kaburburan Ahlul baiti (Allah ya kara musu aminci), da kuma malamai da waliyai, dalilin hakan kuwa shi ne fadin Annabi SallallaHu AlaiHi Wassalam: (Lallai ni na hana ku ziyarar kaburbura, to ku ziyarcesu saboda ziyartansu na kara tunatar da ku lahira), [Muslim] a cikin wata ruwaya kuma: (Na kasance na hanaku abubuwa guda uku, na hanaku ziyarar kaburbura to ku ziyarcesu, saboda a cikin ziyartansu akwai wa’azi da abin lura) [Ahmad].

Idan har ziyarar kabari a asalinsa al’amari ne da aka shar’anta, to lallai nikan gari domin ziyarartan kabari abu ne da aka shar’anta shima, amma fadin Manzon Allah SallalaHu AlaiHi Wasallam: (Ba a nikan gari a tafiya domin ziyara idan ba masallatai uku ba, Masallacin harami, Masallacin Manzon Allah SallallaHu AlaiHi Wasallam da Masallacin Al’aksa) [Anyi ittifaki akansa] abin kebancewa anan shi ne Masallaci ba kaburbura ba, kuma da wuya ka ga wanda zai ce misali: Ni zan tafi ziyarar Masallacin Imam Husain Alaihis Salam ko kuma Masallacin Sheikh Shazili (Allah ya kara masa yarda), abin nufi a wurinsu shi ne ziyartan nagartaccen bawa zuwa kabarinsa, wannan al’amari ne wanda yake ja’izi.

Share this:

Related Fatwas