Bayanin falalar yawan masu yi wa gawa sallah.
Tambaya
Shin yawan wadanda suka sallaci gawa yana nuna falala ne ga shi mamacin?
Amsa
Yawan masu yin sallah ga mamaci alamu ne na samun ceto da gafara ga mamacin, kuma hakan yana nuna samun lada mai yawa ne ga shi wanda ya yi sallar, an karbo daga Dan Abbas Allah ya kara musu yarda ya ce: naji Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam yana cewa: (Babu wani mutum musulmi da zai mutu, sai mutane arba’in su tsaya akansa suyi masa sallah, wadanda ba sa yi wa Allah shirka da komai, face Allah ya basu cetonsa). Muslim.
An karbo daga Uwar muminai Aisha Allah ya kara mata yarda, daga Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya ce: (Wani mutum daga cikin musulmai bai taba mutuwa ba, sai wasu daga cikin al’ummar musulmai suyi masa sallah wadanda ba su kai dari ba, sai su nema masa ceto face an basu cetonsa). Ahmad.