Mallakar kai a ya yin saurin fushi ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Mallakar kai a ya yin saurin fushi da magance hakan.

Tambaya

Ta yaya ya kamata Musulmi ya mallaki kansa a lokacin fushi?

Amsa

Shari’ar Musulunci ta fadakar akan yin fushi, sannan ta yi hani akan yinsa, sai dai fa a inda ya kasance na dalili, sannan ta tunatar da wanda aka jarabta da yin fushi da ya nesanci dalilan da suke haifar masa da haka, wato ya nemi taimakon Allah ya kuma dogara gareshi a cikin dukkan lamuransa, sannan sai ya bi hanyoyin da za su taimaka masa wurin kawar da fushin nasa, kamar neman tsarin Allah daga sharrin shedan la’ananne, sannan ya rinka yin shiru, sannan idan ya yi fushi ya rinka yin alwala, sannan ya rinka canza yanayinsa, kamar zama da mikewa ko kwanciya, sannan ya dabi’antu da halayyar masu yafiya, kuma ya dena saurin fushi, sannan kuma ya rinka danne fushinsa domin ya iya mallakan kansa, sannan kuma yasan cewa fa duk abinda yake furtawa yana rataya ne a wuyansa koda kuwa a halin fushi ya Fada, amma idan wanda yake da saurin fushin ya samu wasu hanyoyi na saukakawa kansa fushin bayan wadanda aka ambata  to babu laifi, a farko da karshe kuma shine ya rinka rokon Allah ya kareshi daga sharrin abinda zai iya cutar dashi. 

Share this:

Related Fatwas