Tsafta da tsarki

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsafta da tsarki

Tambaya

Wani irin muhimmanci ne musulunci ya baiwa tsafta, kuma menene falalar hakan?

Amsa

Musulunci ya kwadaitar da yin tsafta da tsarki ga mabiyansa, inda ya sanya su cikin muhimman abubuwan da suke kunshe cikin sakon da yake dauke da shi, domin ma ya kasance wani yanki ne na imani, sannan ya umurci mabiyansa da su lura da su a kowani sashe, wannan yana zuwa ne sakamakon muhimmancin da ke garesu wurin tsarkake rai da bai wa mutum ikon daukar mauyin  rayuwa. Yana daga cikin muhimmancin da musulunci ke bai wa tsafta kwadaitarwar da yayi a kan tsaftar gidaje da wurare na jama’a tare da tsaftace su daga datti da kazanta, hakanan tsaftar tufafi da fita mai kyau, hakanan tsaftar baki da hakora daga dattin da ke makalewa a ciki, tare dai da sauran abubuwan da ke bayyana a idon kowa.

Share this:

Related Fatwas