Kulawa da motsa jiki
Tambaya
Wadansu abubuwa ne suke nuna muhimmancin da shari'ar musulunci ta ke baiwa lamuran motsa jiki ga kananan yara?
Amsa
Shari'ar musulunci ta kwadaitar da ladabtar da kanan yara, tare da ilmantar da su hanyoyin motsa jiki masu amfani, tare da sauran nau'ukan motsa jiki da suke iya bayyana baiwar da Allah ya basu, da kuma sanin halayyarsu na zamantakewa, wanda yake gina tunanin yaro tun yana karami, sai muga yaro ya taso da tunanin da zai iya taimakawa addininsa da kuma al'ummarsa, daga Abdullahi bin Umar – Allah ya kara musu yarda- ya ruwaito cewa: Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam yace: (Ku koyawa yaranku iyo a cikin ruwa da kuma jifa). Baihaki.