Munana zato
Tambaya
Wanda aka sa mana ranar aure tare yana zargina sosai, to yaya zanyi?
Amsa
Amsa :
Gurbata alakar da ke tsakanin wadanda suke shirin aure da munana zato, ko bibiyan sawunsu domin lalata alakarsu, ya sabawa hikima da kyawun dabi’u na zamantakewa da shari’a ta gina al’umma akansu ga masu shirin aure.
Allah Madaukakin sarki ya hana bayinsa muminai munana zato a wurare da daman gaske cikin littafinsa mai tsarki, daga ciki akwai inda Allah yake cewa : (Ya ku wadanda kuka yi imani ku nisanci yawan yin zato lallai wani sashe na zato zunubi ne ka da ku rinka yin bincike na bin kwakkwafi) {Al’hujirat:12}. Imamu bin Kasir a cikin “tafsirinsa” (7/377 ) : {Allah Ta’ala yana cewa – ai a cikin wannan ayar da ta gabata – yana mai hana bayinsa muminai yawan yin zato, wato zargi da ha’anci a tsakanin ‘yan’uwa da makusanta da sauran mutane ba a inda ya dace ba, saboda wani bangare na hakan yakan kasance sabo ne, to akwai bukatan nesantar yawaita hakan, an ruwaito mana daga Amirul mumina Umar Allah ya kara masa yarda inda yake cewa : {Kada kayi zaton wata kalma da ta fito daga dan’uwanka musulmi face alheri ne, domin kai zaka san gurbin da zaka sanyata wanda ya dace}