Bacewar likkafani da jini
Tambaya
Shin ya wajaba a sake wanke mamaci a likacin da jini ya bata likkafinsa bayan wanka?
Amsa
Bai wajaba ba a sake maimaita wanke gawa ko likkafani sakamakon fitan wani abu daga mamaci bayan an wankeshi, da sanyashi cikin likkafani, abin da akeyi shi ne daukarsa a yanayin da yake ciki domin saukakawa kai wahala bisa ittifakin malamai.
Idan wani abu ya fita daga mamaci bayan wankeshi da sanyashi a cikin likkafani, bai wajaba a shari’ance a sake wankeshi ko canza likkafanin ba, abin da aka shar’anta shi ne a daukeshi a yanayin da yake ciki kamar yanda malamai suka bayyana, saboda sake wanke mamacin akwai tsananin wahala a ciki, saboda sai an sake cire shi daga likkafani sannan a wankeshi sai sake mayar dashi a karo na biyu, don haka ba ace sai an sake yi masa alwala ba sannan a sake canza likkafani, abin da akeyi kawai shi ne a kaishi makwancinsa kawai a yanayin da yake ciki.