Riwayoyin karshen zamani

Egypt's Dar Al-Ifta

Riwayoyin karshen zamani

Tambaya

Yaya kungiyoyin masu kafirta Musulmai suke fassara Hadisan da suka yi Magana akan fitintunu da yake- yake, da kuma irin yanda suke fakewa da haka a matsayin hanyar da za su yaudari mutane?

Amsa

 

Sau da yawa Hadisan da suka yi Magana akan fitintunu da yake- yake bas a dauke da wasu hukunce- hukunce na takalifi, sabanin Hadisan da suka yi Magana akan hukunce- hukunce, manyan dalilai da suka tabbatar da haka sun hada da: Kamanceceniya da dunkule zance da suke sifofin ne na Hadisan da suka yi magana akan fitintunu, mafi yawancin Hadisan da suka yi magana akan fitintunu ba ka raba su da nassi mai rikitarwa (mutashabi), ko kurman nassi da yake a kuruncensa, wadannan sifofi na rikitarwa da kurman baki da suke sifofi ne na mafi yawan Hadisan da suka yi magana akan fitintunu da yake- yake yana bayyana cewa: lallai suna bukatar bayanai; saboda haka ne wahami da kuskure suka yawaita wajen tafsiri da bayanan wadannan Hadisan. Lallai akwai kamanceceniya da take faruwa a zamanin da wasu daga cikin fitintunu, babu kuma wanda ya sansu daidai wadaida sai Allah.. haka ma akwai kamancecenya a mutanen da sunayensu ya gwamu da fitintunun karshen zamani.. saboda haka nunin da aka ya shafe su ne gaba daya.

Lallai da yawa ana samun rudu wajen saukar da ma’anonin wasu daga cikin nassoshin da suka yi magana akan fitintunu akan wasu mutane na musamman, kaman irin yanda ya faru akan ruwayoyi da labaran da suka zo akan Mahdi, da Sufyaniy, domin an sami mutanen da suka fito suke cewa: wane shi ne Mahdi, wane kuma shi ne Sufyaniy, duka wannan soki burutsu ne da ba su da wata hujja, kuma shagaltar da mutane ne da abin da shari’a ba ta nema daga gare su ba.

 

Share this:

Related Fatwas