Kyakkyawan zamantakewa a tsakanin ma'aurata.
Tambaya
Wadan su abubuwa ne suke kyautata zamantakewa a tsakanin ma'aurata.
Amsa
Hukunce hukuncen na shari'a wadanda suka rataya akan rayuwar ma'aurata ba a daukarsu ta fuskar da kowani bangare zai rinka neman madogara na shari'a domin fayyace iyakansa da hakkokinsa da wajibinsa, ta yanda zai rinka yinkurin ganin shi ne yake kan gaskiya a koda yaushe, hakan zai kai ga sanya addini ya zama wani tsani ne na muzgunawa abokin zamantakewa, tare da yi masa matsin lamba wurin yi masa biyayya na dole, wanda kuma hakan na iya sanya mutum ya bar abinda ya wajaba a kansa.
Ana gina rayuwar aure ne akan samun natsuwa da tausayi da kauna, tare da kiyaye mutumcin bagaroran guda biyu fiye da yanda ma shari'a ta bukata ga kowannesu.