Sifanta rayuwar zamantakewar al’umm...

Egypt's Dar Al-Ifta

Sifanta rayuwar zamantakewar al’umma da sifar jahiliyya

Tambaya

Shin samun wasu nau’o’i na sabon Allah a cikin al’umma zai iya sanya al’ummar ta zama al’ummar jahiliyya?

Amsa

Kungiyoyin ‘yan ta’adda sun yi amfani da kalmar jahiliyyar al’umma a cikin tsare- tsarensu, saboda su samu su fake su sifanta gaba dayan al’ummar da ba su akan manhajarsu da kafirci, wannan shi ne ainihin ta’addanci na tunani, saboda su nuna cewa wannan al’ummar al’umma ce ta jahiliyya, koda kuwa sun shaida babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, sun kuma shaida cewa Annabi Muhammadu manzon Allah ne, wannan kuwa abu ne da babu wani daga cikin malaman Musulunci da ya taba fadin haka, in ba wadannan kungiyoyi ba, alal hakika shi Musulunci wani tabbataccen akida ne da ba ya gushewa sakamakon aikata laifi ko sabo, hasali ma irin wannan fahimtar ta yi hannun- riga da abin da Alkur’ani da Hadisai suka zo da su, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Ya Annabi Muhammadu –SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ka ce: Ya ku bayi na da kuka wuce iyaka akan kawunanku, kada ku kuskura ku debe kauna daga rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta zunubai gaba daya..) [az-Zumar: 53], haka ma Madaukakin Sarki yana cewa: (Duk wanda ya aikata mummunar aiki, ko ya zalunci kansa, sannan ya nemi gafarar Allah, to kuwa nan take zai sami Allah mai yawan gafara da rahama ne) [an- Nisa’i: 110], Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Asalin da tushen imani guda uku ne: la’ilaha illalLahu, da kada mu kafirta shi saboda aikata zunubi, da kuma kada mu fitar da shi daga Musulunci sakamakon wani aiki da ya yi) [Abu Dawud], sam bai halatta wani ya jefi al’ummar Musulmai da kalmar jahiliyya saboda ana aikata sabo ba, yin hakan abu ne da ya saba da abin da shari’a ta zo da shi.

Share this:

Related Fatwas