Yin fidiya ga wanda ya rasu akwai azumi akansa saboda rashin lafiya.
Tambaya
Shin ya halatta a yi fidiya ga wanda ya rasu akwai azumi akansa saboda rashin lafiya?
Amsa
Wanda ya sha ruwa saboda da rashin lafiya, ya kuma sami daman biya bai yi ba, wajibi ne a fitar masa da fidiya daga dukiyar da ya bari a cikin sulusin wasiyya idan ya yi wasiyya akan haka, idan kuma bai yi wasiyya ba mustahabi ne a fitar masa ta bangaren tabarru’i.
Wanda ya sha ruwa a watan Ramadan saboda rashin lafiya; to wajibi ne ya rama idan rashin lafiyar ya gushe, rashin lafiya daya ne daga cikin uzurorin da suke halatta shan ruwa, idan rashin lafiyar zai cutar da jiki, ko ya yi sanadiyyar jinkirin waraka, to a irin wannan yanayi wajibi ne mara lafiyan ya sha ruwa, wanda ya sami dama bayan ya warke, amma bai ram aba har ya rasu, wajibi ne a fitar masa da fidiya daga cikin sulusin da aka kebance domin yin wasiyya a cikin dukiyar da ya bari, idan ya yi wasiyya da yin haka, idan kuma bai yi wasiyya ba, mustahabi ne a fitar masa ta hanyar tabarru’i daga koma wane ne; shin yana cikin magada, ko bay a ciki, ba za a fitar daga cikin gado ba, sai idan dukan magada sun amince a fitar daga cikin gado kafin a raba.