Sayar da magungunan da aka tanaza d...

Egypt's Dar Al-Ifta

Sayar da magungunan da aka tanaza domin inshoran lafiya.

Tambaya

Akwai wasu masu kemis da suke sayar da wasu magunguna a kemis dinsu wadanda aka tanaza domin inshorar lafiyar mutane, amma suke sayarwa ga wadanda ba don su aka tanaza  ba, mene ne hukuncin haka?

Amsa

Su magungunan da aka tanaza domin inshorar lafiyar mutane ba hakki bane da za a nemi riba akansu, sai dai ana bayar da su ne ga marasa lafiyan da aka tanaji magungunan domin ayi musu allura a daidai lokaci, domin hukuma ce take biyan kudin magungunan, sannan an shardantawa wadanda suke amsar magungunan da kada su sayar da su, domin kudinsu hakkin al’umma ne, bai kamata ayi tasarrufi a kayan al’umma ba sai dai bisa doka da ka’idoji, a bisa haka bai halasta ayi mu’amala da magungunan ba ta fannin saye ko sayarwa, bugu da kari kuma wannan yana cutar da harkar lafiya a cikin al’umma ta hanyar barna da wuce gona da iri akan hakkin marasa lafiya.

Yin hada-hada a wannan harka ko taimakawa a cikinsa ta hanyar wasu masu kemis ko waninsu da aka amince dasu wurin isar da hakkin ga masu shi yana zama ha’inci ne, duk mai aikata hakan ya cancanci horo da ukuba ranar alkiyama, tare da gurfanar da mai aikata hakan agaban kotu domin yi masa shari’a.

Allah Madaukakin sarki ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas