Rashin bibiyan lokacin al’ada sakam...

Egypt's Dar Al-Ifta

Rashin bibiyan lokacin al’ada sakamakon rashin lafiya

Tambaya

Mace mara lafiya da ake yi mata magani ta hanyar “chemotherapy”, wadda hakan yakan lalata tsarin kwanakin al’adarta, yaya za ta lissafa kwanakin al’adar tata?

Amsa

Idan mace ta ga jini kafin wucewar kwanaki goma da yin tsarkinta na al’adar da ta gabata: to wannan jinin na rashin lafiya ne, amma idan ta ganshi bayan wucewar kwanaki goma, ko sama da goma: to wannan jinin al’ada ne idan ya kasance ranaku uku da dararensu, ko sama da haka, matukar dai bai wuce kwanaki goma ba, kuma ya zama hakan ba al’adarta ba ne, amma idan ya gaza ranaku uku da dararensu: to jinin na rashin lafiya ne, idan kuma ya zarce kwanaki goma; idan tana da wani abu sananne da ta saba da shi da bai kai kwanaki goma ba, sai ta mayar da shi zuwa ga abin da ta saba da shi, abin da ya karu akan hakan sai ya zama na rashin lafiya ne, a irin wannan hali dole ne ta rama sallolin da suka kubuce mata na kwanakin da suka karu akan yanda ta saba. Amma idan ba ta da wata al’ada da ta saba da shi; to kwanakin al’adarta ana kaddara su ne da kwanaki goma, duk abin da ya karu akan haka jinin rashin lafiya ne, sai ta yi wanka bayan wucewar kwanaki goma, amma idan jinin ya cigaba da fito mata, to za ta lissafa al’adarta ne bayan kowane wata sai ya zama lokacin ne lokacin al’adarta, abin da ya rage a cikin watan kuma shi ne lokacin tsarkinta, matukar ta san lokacin al’adar nata da kididdigar kwanakin, ta san farkon lokacin farawarsu da lokacin karewa, amma idan ba ta da wani sanannen abu da ta saba da shi: sai a mayar da ita zuwa ga mafi yawan kwanakin al’ada watau kwanaki goma, sai ya zama tana yin al’ada ne na tsawon kwanaki goma, abin da ya karu akan haka kuma ya zama jinin rashin lafiya, duk kuma lokacin da aka tabbatar da cewa jinin na rashin lafiya ne, to duk abin da ya haramta ta aikata a lokacin al’ada ya zama halal ne ta aikata shi irinsu: sallah da azumi da sauransu idan ta yi wankan tsarki, ya kamata a san cewa wannan takadirin ya kebanta ne kawai da hukunce- hukuncen ibada na sallah da azumi da makamantansu, ba wai da hukunce- hukuncen al’ada ba.

Share this:

Related Fatwas