Cika kudin abubuwan bukatar talakaw...

Egypt's Dar Al-Ifta

Cika kudin abubuwan bukatar talakawa daga cikin kudin zakkah

Tambaya

Mene ne hukuncin cike kudin abubuwan bukatuwar talakawa kamar su nama da kaji daga cikin kudaden zakkah?

Amsa

Ya halasta ga kungiyoyin taimakon al’umma su rinka ware wani kaso daga cikin kudaden zakkah matukar hakan shine mafi dacewa ga su mabukatan, su kungiyoyi na taimakon al’umma kamar wakilai ne na mabukata wurin siyan ababen bukata, idan aka lura da bukatar su mabukatan ta fuskan gabatar da abinda yafi dacewa dasu, to babu hani a shari’ance wurin sanya wani sashi na irin wadannan abubuwan a matsayin abubuwan da suke bukata gwargwadon abinda zai wadatar da kowani iyali, wato dai hakan yana nuna an fitar da zakkar kenan ta hanyar bayar da kayan bukata matukar anga dacewar hakan bisa la’akari da bukatun mabukata tare da biyan abubuwan bukatarsu, hakanan kuma wannan yana iya zama ta fuskar fitar da zakkah ta hanyar baiwa mabukata da talakawa abinda suke bukata.

Share this:

Related Fatwas