Asalin dangantaka tsakanin malamai ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Asalin dangantaka tsakanin malamai da masu mulki

Tambaya

Mene ne asalin dangantakar da ke tsakanin malamai da masu mulki?

Amsa

Asalin  dangantaka tsakanin malamai da masu mulki shi ne biyayya ta bangaren malamai kasancewarsu a matsayi na farko daga cikin talakawa, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ku yi Allah biyayya ku bi Manzon Allah tare da shugabanninku) [An-nisa’i: 59], sannan sai yin nasiha, domin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Shi wannan addinin nasiha ne), sai muka ce ga wa? Sai ya ce: (Ga Allah da littafinsa da Manzonsa da kuma shugabannin Musulmai da gama garinsu) [Muslim], ya wajaba ga malamai su lizimci dokoki da ladubban yin nasiha ga shugabanni, yana daga cikin abin da aka samo daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda yake son yi wa mai mulki nasiha, to kada ya bayyana hakan a fili, sai dai ya kamata ya rike hannunsa su kebance don yi masa nasiha, idan ya amshi nasihar, to madallah, idan kuma bai amsa ba to shi dai ya isar da abin da za iya wanda ya wajaba akansa) [Ibn Abi Aseem]. Amma a bangaren mai mulki a duk lokacin da ya samu ra’ayi na kwarai da shawara mai amfani da nasiha mai kyau, to shi ne mafi dacewa da ya dauka, hakika Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ka shawarce su a cikin al’amura) [Ali Imran: 159]. An ruwaito daga Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Kalmar ta hikima abun mumini ne wanda ya bata, a duk inda ya same kayansa to shi ne mafi dacewa da shi) [Tirmizi].

Share this:

Related Fatwas