Asalin yanda dangantaka take tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba.
Tambaya
Mene ne asalin yanda dangantaka take tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba?
Amsa
Amsa :
Asalin yanda dangantaka take tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba shi ne: aminci, da zaman tare, da sanayya domin amfanar da dan Adam, ita kalmar asali cikin kalma daya anan tana nufin “kyautatawa” Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Allah bai hanaku yin dangantaka ko mu’amala da wadanda ba su yake ku ba saboda addininku, sannan ba su fitar daku daga gidajenku ba, to Allah bai hana ku yi musu da’a, ko ku kyautata musu ba, domin Allah yana son masu kyautatawa) [Al-mummtahina: 8], kalmar “kyautatawa” anan ba ta nufin “adalci”; saboda shi Musulmi abin umurta ne da yin adalci, ko ga makiyansa ne, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Lallai kada tsananin laifin wasu mutane ya hana ku yi musu adalci ku yi adalci shi ne mafi kusance da tsoron Allah) [Al-ma’idah: 8]. To abin nufi anan shi ne da’a “al-bir”da kyautatawa, duk da haka idan aka lura za a ga Allah bai hana Musulmai kyauatatawa abokanan gaba masu yakansu, ai kyautata musu ma sunna ce, sai dai Allah ya hana Musulmai yi musu biyayya da karkata zuwa gare su ne, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Sai dai Allah ya hane ku ne da yin da’a ko kyautatawa ga wadanda suka yake ku saboda addininku, sannan suka fitar da ku daga gidajenku sannan suka bayyana cewa sun yake ku sun kuma kore ku daga gidajenku kan yi karkata zuwa gare su) [Al-mumtahina: 9], muna iya ganin hakan a zahiri cikin rayuwar Al-mustapha (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cikin Hadisai masu yawa, kamar dai Hadisin Al-Akhshabaini, da sulhun Hudaibiyya, da Hadisin dulaka’i da waninsu.