Saba wa dokokin kasa da kasa bayan ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Saba wa dokokin kasa da kasa bayan amincewa da hujjar cewa an kulla su ne da wadanda ba Musulmai ba.

Tambaya

Shin ya halasta a saba wa dokokin kasa da kasa bayan amincewa da hujjar cewa an kulla su ne da wadanda ba Musulmai ba?

Amsa

Bai halasta a saba wa dokokin kasa da kasa bayan amincewa da hujjar cewa an kulla su ne da wadanda ba Musulmai ba; saboda Allah ya ce: (Ku cika alkawari lallai shi alkawari abin tambaya ne) [Al-isra’i: 34], Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Wanda ya kasance akwai alkawari tsakaninsa da wasu mutane, to kada ya janye alkawarin, ko ya warware har sai lokacin yarjejeniyar ya cika) [Abu Dauda]. Hakika Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kulla alkawari tare da Yahudawa a Madina wanda a yanzu za mu iya kiran alkwarin da sunan “yarjejeniyar tsaro na hadaka da taimakekeniyar tattalin arziki” yana daga cikin abin da ya zo cikin yarjejeniyar cewa: (Lallai ne Yahudawa su rinka ciyarwa tare da muminai matukar sun kasance a halin yaki.. sannan ba sa tare da ‘yan kasuwan Kuraishawa, ko wanda yake taimaka musu, sanna kuma za su taimaka wurin kare Madina a duk sanda aka kawo mata hari) sai dai fa Yahudawa sun warware alkawarin da aka yi da su kamar yanda aka sani, haka nan Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kulla yarjejeniya tare da mushirikan Makkah wanda sahabbai suka kalli wannan yarjejeniyar a matsayin an zalunce su a ciki, wato dai sulhun Hudaibiyya kenan, amma duk da haka warware yarjejeniyar ya kasance ne ta bangaren mushirikan, har wala yau, yana daga cikin abin da aka sani cewa su Yahudawa da mushirikai sun kasance mafi nuna kiyayya ga Musulmai a wancan lokacin.

 

Share this:

Related Fatwas