Asarar da aka samu ta hanyar Hawari...

Egypt's Dar Al-Ifta

Asarar da aka samu ta hanyar Hawarijawan zamani ta fuskar lamuran yau da kullum da zamantakewa da na addini a ƙasar Misra.

Tambaya

Ta yaya Hawarijawan zamani suka yi ɓarna kuma suka cutar da al’umma ta fuskar lamuran yau da kullum da zamantakewa da na addini a ƙasar Misra?

Amsa

Manhajin Hawarijawan wannan zamanin ya keɓanta da wasu munanan tunani da suka ruɗar da mutane da su akan cewa suna daga cikin addini, daga ciki akwai yawan fito- na- fito da hukumomi bisa raya cewa dukkan hukumomin ƙasashen Musulmai a yau hukumomi ne – a mafi ƙaranci – a ce musu ɗagutai ne, idan har ba a kira su da kafirai ba, wai ba a aiwatar da shari’a a ƙasashenmu, kuma duk malaman shari’a da suke aiki a ƙarƙashin gwamnatoci malaman gwamnati ne ba na Allah ba, domin wai sun sayar da addininsu da duniyarsu, tare da yaɗa zantuttukan ƙarya da na shaci - faɗi waɗanda za su iya tayar da wutar fitina a tsakanin Musulmai da wasunsu da suke zaune a ƙasa ɗaya, haƙiƙa wannan fahimtar ta bayyana ɓaro- ɓaro cikin ayyukan wasu da suka bi layinsu suka gasgata su, domin a cikinsu akwai masu halatta kuɗin jama’a da sunan ana zalunci, ko kuma saboda kafircin hukumomi, kuma ba sa neman sani, ko haske daga malaman da suke aikin gwamnati, ko suke aiki ƙarƙashin gwamnati, ai koda yaushe ma sukansu  suke yi, sannan suna bayyana ƙiyayya da ƙyashinsu ga ƴan’uwansu mutane da zaman ƙasa ɗaya ya haɗa su tare, ba sa yin mu’amala tare da su, da dai sauran abubuwan da suka yi nesa da koyarwar ingantaccen addini da kyawawan halaye.

Share this:

Related Fatwas