Karkasuwan duniya zuwa gida zaman l...

Egypt's Dar Al-Ifta

Karkasuwan duniya zuwa gida zaman lafiya da gidan yaki tare da dalilin hakan.

Tambaya

Menene ma’anar gidan zaman lafiya da gidan yaki, shin akwai abinda ke tabbatar da wannan kashe-kashen daga Alkitabu ko kuma Sunnah?

Amsa

Tunanin mafi yawa daga cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda kan tsaya ne akan mummunar fahimta wanda yake karkatacce wanda ya kunshi wasu tarin hukunce hukunce dake da alaka da ma’anoni, daga ciki akwai ma’anar gidan yaki da gidan zaman lafiya, wadannan abubuwa ne dake da alaka da juna,  don haka rarraba gidaje zuwa ga na zaman lafiya da kuma yaki ya tattara lamarin hijira da jihadi.

Ana lura da cewa karkasa kasashen duniya zuwa ga kasashen musulmai da na wadanda ba musulmai ba daya ne daga cikin muhimman abubuwa dake da alaka da siyasa a fikihu, saboda hakan wannan yana da alaka da nazarin addinin musulunci bisa alakarsa da jihadi, haka kuma ya kunshi hukunce hukuncen mutane mafiya karanci na addini saboda hakan shine dalilin nazarin fikihu bisa alaka ta kasa da kasa da yake tattare dashi.

A cikin kur’ani ko a Sunnah Mai tsarki babu wani abu mai nuni zuwa ga karkasuwan kasashen duniya bisa Imani da kafirci ko yaki da zaman lafiya,  kololuwar abinda ke cikin haka shine wannan kashe kashen ba wani abu bane face mahanga ta fikihu akan zahirin alakar dake tsakanin musulmai da wadanda ba musulmai ba, domin yaki kan kasance ne kawai yayin da aka rasa yarjejeniyar zaman lafiya, don haka wannan rabe raben anyi ne domin kallon yanayin da ake ciki ba wai tsarin shari’a ba, manufar hakan baya nuna sanya duniya bisa tsarin hukuncin kasashe biyu, ko kuma bangarori biyu na siyasa, bangare daya ya kunshi kasashen musulmai, kuma gwamnati ke shugabantarta, dayan kuma ya kunshi kasashen da ba na musulmai ba, kuma gwamnati daya ke mulkanta, kawai dai wannan rabe raben anyisa ne bisa samuwar tsaro da zaman lafiya ga musulmai a kasashensu, tare da samuwar tsaro da hari a kasashen da ba na musulmai ba.   

Share this:

Related Fatwas