Hukuncin yin sujuda na tilawa ga wanda bai da alwala.
Tambaya
Mene ne hukuncin yin sujuda na tilawa ba tare da alwala ba?
Amsa
Ita dai sujada na tilawa a wuraren yin ta cikin Alkur’ani Maigirma sunna ce mai karfi, a wurin mafi yawan malaman fikihu, kama daga Malikiyya da Shafi’iyya da Hambaliyya, ga mai karantawa da kuma mai sauraro, don haka ana sakawa wanda ya yi sujadan, kuma ba a zargin wanda bai yi ba, amma an shardanta yin tsarki daga babban hadasi da karami ga wanda zai yi wannan sujadan, kamar dai yanda jumhorin malamai suka tabbatar, irin su Hanafiyya da Malikiyya da Shafi’iyya da kuma Hambaliyya, saboda sujada sallah ne, ko kuma wani aiki ne da yake da ma’anar sallah, ita kuma sallah ba ta inganta sai da tsarki, saboda abinda Abdullahi bin Umar ya ruwaito, - Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa- ‘yace: Mutum ba ya yin sujada face yana da tsarki,’ Imam Malik ya fitar a Mawadda, Al-Hafeez ibn Hajr kuma a Fathul Bari, (554/2), sannan yace: isnadin wannan hadisin ingantacce ne.
Ambaton Allah ya na da yalwa ga wanda bai yi sujada ba saboda wani uzuri ka da kuwa yana da tsarki, kamar dai yace; Sunhanallahi wal hamdu lillah, wa la ilaha illallah wallahu Akbar, so (hudu)