Hukuncin yin sakaci da aiki da kuma kwadaitarwa akan kulawa da yin aiki.
Tambaya
Ta yaya Musulunci ya yi gargadi kan yin sakaci da aiki tare da kwadaitarwa akan kulawa da yin aiki tukuru?
Amsa
Shi ma’aikaci ko mai aiki idan ya yi sakaci da aikinsa da aka dora masa alhakin yi to ya nuna akwai ha’inci a cikin aikinsa kenan, kuma wannan yana daga cikin algus da makirci da zambo, saboda shi wannan ma’aikacin amintacce ne akan aikin da aka bashi, don haka rashin aiwatar da aikinsa kamar yanda ya kamata – Tare da amsar albashi akan aikin – to wannan wuce gona da iri ne, kuma bai halasta ba.
Hakanan wannan irin aikin ya sabawa tsarin hukumar gudanarwa na ayyuka, kuma hukumar ta na ladabtar da mai tawaye aikinsa, abinda ake so shine a kwadaitar da ma’aikaci mai yin aikinsa tsakani da Allah kan cewa zai samu lada akan aikinsa da yake yi, matukar ya cigaba da yin aikinsa tsakani da Allah tare da yin kokari wurin kiyaye martaban aikin.