Hukuncin fitar da zakka tare da cire kudaden haraji daga riba
Tambaya
Wane lokaci ne ake fitar da zakka a dukiyar kasuwanci, da hukuncin cire kudin haraji daga riba?
Amsa
Abin da shari’a ta tabbatar shi ne wajibi ne gad an kasuwa ya kebance hajarsa da dukiyarsa ta asali da ribarsa, ya fitar wa duka da zakka, da sharadin shekara ta kewayo, ba a cire harajin da gwamnati take amsa akan ribar da ya samu; domin hakkin gwamnati ba zai hana a fitar da hakkin Allah ba, ana fitar da haraji ne daga cikin dukan dukiya kafin a fara lissafin zakka.