Hada niyyar yin azumi tsakanin ramuwa da kuma azumin kwanaki shida na Shawwal.
Tambaya
Mene ne hukuncin hada niyyar azumi na ramuwa tare da azumin kwanaki shida na watan Shawwal?
Amsa
Ya halasta ga Musulmi ya yi niyyar yin azumin nafila tare da niyyar rama azumin farilla, sai ya rama abinda ake binsa na azumin watan Ramadan a watan Shawwal, sai ya wadatu da azumin da yake yi a duk ranar ramuwa tare da niyyar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, don haka zai samu lada kashi biyu kenan, amma mafi cika da dacewa shine mutum ya azumci kowanne daban.