Sayen kayayyakin bukata ga wadanda ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Sayen kayayyakin bukata ga wadanda suka cancanci zakka na kudi.

Tambaya

Shin ya halasta a bayar da wani sashe na zakkar kudi wurin sayen kayan masarufi domin rabawa talakawa da mabukata.

Amsa

Asalin zakka dai ana fitar da ita ne daga kudin ya kai nisabi, amma Hanafiyya sun halasta a fitar da kimar abin kudin idan har hakan yafi wadatar da mabukatan, domin haka, fitar da wani sashe na zakkan kudi ta hanyar sayen kayan masarufi domin baiwa talakawa da mabukata abu ne wanda ya halasta a shari'ance, kuma babu laifi idan aka yi hakan, sai dai ya kamata shi mai fitar da zakkan ya lura da abinda yafi amfani ga mabukata sai ya fitar da zakkar dashi. 

Share this:

Related Fatwas