Samar da kudaden gudanar da ayyuka ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Samar da kudaden gudanar da ayyuka ta hanyar bankuna.

Tambaya

Mene ne hukuncin Samar da kudaden gudanar da ayyuka ta hanyar bankuna?

Amsa

Cinikin da aka kulla kan samar da kudaden bunkasa tattalin arziki tsakanin bankuna da hukumomi ko kungiyoyin al’umma a bangare guda, sannan a daya bangaren a kulla cinikin da daidaikun mutane ko wasu hukumomi a zahirin gaskiya ciniki ne da ake ginawa akan sanin aikin da za ayi tare kudin da za a kashe da kuma ribar da za a samu, wanda zai kasance babu rudu da cutarwa, kuma ya zama duka sassan biyu ko bangarorin biyu za su amfana da ribar da za a samu, to irin wannan cinikin halas ne a shari’ance domin babu kamai, kuma bai kamata ma a ambaci irin wannan cinikin a matsayin bashi ba, saboda maganar bashi ana dorasa ne akan tausayawa da taimako, shi wannan yana daga cikin cinikin abinda aka bayar domin taimako, irin wadannan cinikayyan da bunkasan arziki na mayar da abinda aka amsa, don haka idan aka ambaci irin wannan cinikin a matsayin “bashi” zai haifar da rudani wurin fayyace ka’idar bashi, wanda matukar aka samu riba a cikin bashi to ya zama riba.

Share this:

Related Fatwas