Kawar da cuta ake gabatarwa akan ne...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kawar da cuta ake gabatarwa akan nemi amfani

Tambaya

Shin da gaske yakar wadanda ba Musulmai ba a yanzu jawo amfani ne Kaman yanda kungiyoyin yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi suke yayatawa?

Amsa

A cikin ka’adojin da suke tabbatattu ne a cikin shari’ar Musulunci akwai ka’idar: “Kawar da cuta ake gabatarwa akan jawo amfani”, lallai wannan ka’ida ce mai matukar muhimmanci, domin dukan ayyukan mutane ba za su fice daga tsakananin maslaha da barna na, saboda haka dole a yi aiki da wannan ma’auni na gaskiya, da sanya komai a gurbin da ya dace da shi, saboda abin da yake da rinjaye ya rinjaya. A asali ana gabatar da kawar da cuta akan jawo amfani, a cikin dalilan da suke tabbatar da haka akwai inda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya Annabi Muhammadu (SallalLãhu alaiHi wa aliHí wa sallam), suna tambayarka game da hukuncin giya, da cãcã, to, ka ce masu: lallai a cikinsu akwai cutarwa mai yawa na lalata lafiya, da tafiyar da hankali da dukiya, da haifar da kiyayya, da ta’addanci tsakanin mutane, haka ma a cikin su akwai amfani da wasu bangare na amfanin lafiya, da samun riba cikin sauki, sai dai fa cutarwarsu tafi amfanin yawa, don haka ku nesance su. Suna tambayar ka kan abin da za su ciyar, amsa masu da cewa: su ciyar da abu mai sauki, kuma kadan wanda ba zai wahalar da su ba, su yi haka saboda Allah, ta haka ne fa Allah yake bayyana maku ayoyi, ko za ku yi tunani akan abin da amfaninsa zai dawo maku a cikin maslahohin duniya da lahira) [al- Bakra: 219].

Abin da ake nufi a nan lallai giya da caca suna da amfani ga wasu mutane, amma duk da haka akan haramta su sakamakon yawan cutarwar da suke cikinsu.

Lallai wannan ka’ida ta “kawar da cutarwa ake gabatarwa akan jawo amfani” ta shahara a wurin malamai masana Fikihu, idan an sami cin karo tsakanin barna da amfani, sai a fara da kawar da barna; saboda shari’a ta fi muhimmanta abubuwan da aka hana akan abubuwan da aka bayar da umurnin a aikata, saboda haka ne mai tsira da aminci ya ce: (Idan na umurce ku da wani abu, to ku aikata shi gwargwadon ikonku, idan kuma na hana ku wani abu, to ku nesance shi kawai).

Shi jihadi ta wannan hanya a yanzu –idan ma fa mun yarda cewa hakan jihadi ne, domin aikinsu a hakika shi ne ainihin ta’addanci- a mafi yawan lokaci yana tare da kafirta shugabanni, sannan kuma yana bata sunan Musulunci da hukunce- hukuncensa da ma mabiyansa, abin da yake kai wa zuwa ga barna da cutarwa masu yawa, ma’ana haka zai jawo wa Musulmai yake- yaken da ba za su iya, inda hakan yake tabbatar da cewa barnar da yake cikin haka ya fi amfanin yawa.

Share this:

Related Fatwas