Kasuwanci a kafafen sadarwa na zamani.
Tambaya
Mene ne hukuncin yin ciniki ta hanyar intanet?
Amsa
Yin amfani da kafar intanet wurin saye da sayarwa wanda akafi sani da (cinikayya ta kafar yanar gizo), to halas ne a shari’ance, saboda wananan ya shiga cikin tsarin siyayya da kasuwanci da yake cikawa mutane muradinsu, amma ya zama da sharadin gushewar garari da cutarwa da kuma rufa-rufa akan abin saye ko sayarwa, tare da bin dokoki da ka’idojin kafofin da suke sanya wannan tsarin na kasuwanci.