Kasuwanci a sashen kayayyakin tarihi
Tambaya
Mene ne hukuncin sayar da kayan tarihin da ake hakowa, da kuma cinikayya a kansu baki daya?
Amsa
Bai halasta ba a shari’ance a yi kasuwanci da kayayyakin tarihi ko tasarrufi a cikin kayayyakin kamar sayarwa ko kyauta ko wani abu makamancin haka, domin haka na daga cikin tasarrufin shugaba ne, sannan ya zama ya aminta da shi, kuma ya zama doka ta tsara yanda za a taimaka wurin samun alfanun al’umma daga kayayyakin, wannan kuwa koda mutum a filin da ya mallaka ne ya samu kayan tarihin, domin mallakan filin ba ya halasta mallakan abin da aka samu a karkashin filin na kayan tarihi, sai dai fa idan wanda ke mallakar filin ya gaji kayan tarihin ne daga mai asalin filin, - wanda hakan ba mai yiwuwa bane – kai ba abin da ke iya tabbatar da hakkin mallaka ko da kuwa ya tabbata shi wanda ya samu kayan yana da gadon mai asalin wurin na farko, wannan kuma na zuwa ne bisa dalilai ma su yawa, idan har aka samu rashin yiwuwar hakan a yanayin da ya gabata, shin kayan ya kasance kudi ne ko kaddara ne daban, to abun ya zama tsintuwa kenan dole a komar da shi zuwa ga gwamnati, to wannan shi ne fahimtar hukumar bayar da fatawa ta kasar Masar td ta ke akai, hakanan ma’aikatar shari’a.
Allah Madaukakin Sarki shi ne mafi sani.