Cinikin kayayyakin tarihi

Egypt's Dar Al-Ifta

Cinikin kayayyakin tarihi

Tambaya

Mene ne hukuncin sayar da kayan tarihi ko waninsa da mutane ke tsinta ko tonowa, tare da yin kasuwanci a cikin wannan harkan gaba daya?

Amsa

Bai halasta ba a shari’ance ayi kasuwanci a harkar kayan tarihi ko yin amfani da kayan ta hanyar bayar da su kyauta, ko wani abu mai kama da haka na tasarrufi ba tare da bin ka’ida ba, wanda hakan shi ne ya kasance bisa dokokin da zai sanya kowa ya amfana da abin da aka samo ko aka hako ko aka tsinta, ko kuwa mutum ya tsinci kayan ne a filinsa, mallakar fili ba ya halasta mallakan abin da ke karkashin kasar ga mai shi, matukar shi wanda aka tsinci kayan a filinsa ba ya kasance daya ne daga cikin magadan wanda ya bar kayan tarihin ba, - kuma hakan abu ne mai wuyan gaske a yau – kai hakkin mallaka ma ba ya tabbata koda kuwa ga magajin asalin mai kayan ne, saboda wasu dalilai masu yawa, idan har aka rasa hanyar ciruwar mallakan zuwa ga wani ta hanyoyin da aka ambata a baya, to duk abin da aka samu hakkin kowa da kowa ne, kuma abin tsintuwar ya zama na gwamnati, kuma dole a mayar mata, abisa wannan fatawar ne Hukumar bayar da fatawa ta kasar Masar take akai da hukunci.

Allah Ta’ala ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas