Jahadin da yake cikin littattafan tarihi
Tambaya
Shin fahimtar jahadi kamar yanda yake a cikin littattafan tarihi na daga cikin tabbatattun tsare- tsaren shari’a, ko kuma hakan yana daga cikin babi ne na fahimtar da take iya sauyawa?
Amsa
Fahimtar jahadi yana nan a cikin littafan tarihi daga cikin babin fahimtar abubuwan da ka iya sauyawa bisa ijitihadin malamai, wato dai shi ba wani abu ne da yake matabbaci wanda ba ya sauyawa daga cikin fahimta ko fikihun jahadi ba, abin da ba ya sauyawa kawai shi ne asalin shar’anta shi, domin ya tabbata ne a matsayin wata hanya daga hanyoyin kare kai daga zaluncin azzalumi da ta’addancin mai ta’addanci kamar yanda nassin Al-kur’ani mai girma da Sunnar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) suka tabbatar, daga cikin ayoyin hakan akwai inda Allah mai girma yake cewa: (An yi umurni ga wadanda ake yakarsu lallai an zalunce su, kuma lallai Allah mai cikakken iko ne akan ya ba su nasara) [Al-haaj: 39], daga cikin Hadisai kuwa akwai wanda aka ruwaito daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) lokacin da aka tambaye shi: Wani aiki ne mafifici? Sai ya ce: (Imani da Allah da jahadi FisabilillaHi) [Al- Bukhari da Muslim], sannan halaccin yin jahadin yana rataye ne da sharuddansa da aka cimma yarejejeniya kawai tsakanin malaman fikihu, wato kasancewarsa cikin tabbatattun abubuwan da aka shar’anta, kamar dai samuwar Imamu da amincewarsa, amma sasanninsa wanda ya kunshi kamannin aiwatar da jahadin a zahiri, to shi ne bangare mafi girma daga cikin hukunce hukuncen jahadi, wanda kuma ya kasance daga cikin hukunce hukuncen da suke iya sauyawa bisa ijitihadin masanin fikihu ta hanyar la’akari da sauyawar lamura da lokuta da yanayin da aka tsinci kai a cikinsa, abin da ke saita wannan lamarin shi ne hangen nesan majibincin al’amarin Musulmai (shugaba) da kuma yanda yake gudanar da siyasar mulkinsa.