Alamomin nuna tsauri cikin lamuran ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Alamomin nuna tsauri cikin lamuran da suka faru a tarihi

Tambaya

Shin ko zaku iya ambata mana misali daga cikin ire-iren tunani mai zafafa kishin addini a tarihin Musulunci?

Amsa

Shi tarihin musulunci a cike yake da abubuwan da za su iya sanya masu ra’ayi mai tsauri daukar wani bigire a cikinsa domin daukan tunani ko wani aiki mai tsauri, hakika anci gaba da mu’amala da irin haka da kokarin magance wannan matsala cikin hikima da nuna kwarewa sosai, daga cikin akwai kissar mutane ukun da suka zo gidan Annabi SallaLaHu AlaiHi wasallam, da aka basu labarin irin yanda yake ibadarsa sai suka raina yanda su suke nasu ibadar, sai suka ce: Ina mu ina Annabi SallaLaHu AlaiHi wasallam bayan shi an gafarta masa zunubansa wanda ya gabatar da wanda ya jinkirta, sai na farkonsu ya ce: “Ni zan ta yin sallah kullum ba kakkautawa” sai wani cikinsu ya ce: “ Ni kuma zan ta yin azumi ba fashi” sai na karshen ya ce: “ Ni kuma zan kauracewa mata, ba zanyi aure ba har abada” sai Annabi SallaLaHu AlaiHi wasallam ya zo garesu ya ce: “Ku ne wadanda kuka ce kaza da kaza, to Wallahi na fiku tsoron Allah da yi masa bauta, amma ni ina yin azumi kuma ina shan ruwa, na kanyi sallah kuma nayi barci, sannan kuma ina auren mata, to fa duk wanda ya kauracewa sunnata to ba shi tare da ni, wato baya kan tafarkina”.

Daga cikin misalan tsanantawa a wannan zamanin kuwa shi ne: yanda wasu kungiyoyi suke kokarin cusa tsanantawa a cikin lamuran addini, inda suke kokarin sanya haka a matsayin wata alama kebantacciya da tambari na su na kashin kai, kamar dai haramta wasu bukukuwa wadanda wasu daga cikinsu ma addini ya kwadaitar da yin irinsu, kamar dai bukin maulidin Annabi mai girma, ko kuma babu wani dalilin shari’a da ya zo ya haramta yin hakan, kamar haramta ranar uwa ta duniya, da na shiga lokacin kaka, da dai sauran abubuwa irin haka, wadanda shari’a ba ta zo ta haramta yinsu ba karara.

To irin wadannan kungiyoyin suna kokarin raunata nagartattun abubuwa na musamman akan wayewar da yake tattare da tushen Addini, alhalin kuwa sune mafi nesa da koyarwar da ke cikin tushen addini.

Share this:

Related Fatwas