Aibobi a jariran da suke cikin mahaifa
Tambaya
Mene ne hukuncin yin amfani da na’urorin zamani wajen gano wasu aibobi da suke tattare da jariran da suke cikin mahaifa da yi masu magani?
Amsa
Yin amfani da hanyoyi na zamani domin gano aibobin da suke kama gabobin jiki a lokacin da jariri yake cikin mahaifar uwa abu ne da shari’a ta bayar da izini, matukar wadanda za su yi haka likitoci ne kwararru a wannan fage, za a hana ne kawai idan ana da tabbaci, ko a mafi rinjayen zato cewa hakan zai kai zuwa ga cutar da uwa ko jaririn, to a nan sai shari’a ta hana.
Haka ma na’urorin zamani da ake amfani da su wajen magangace cututtukan jarirai a cikin mahaifa, sawa’un ta hanyar shigar da magani ne, ko kuma yi masa aiki, shari’a ba ta hana ba, sai idan an tabbatar da cewa hakan zai cutar, ta yanda zai zama cutar da hakan zai haifar ya fi cutar da ake son a warkar.