Kwadaitarwar shari'a game da tsafta...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kwadaitarwar shari'a game da tsaftar jikin dan Adam

Tambaya

Ta yaya shari'a ta kwadaitar game da tsaftar jikin dan Adam?

Amsa

Shari'ar Musulunci ta kwadaitar game da tsaftace baki da hakori ga barin sauran abinci da yake cutar da lafiyar dan Adam; Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ba domin kada in tsananta wa al'ummata ba, da na umurce su da yi asuwaki a lokacin kowane sallah) [al- Bukhari], ta kuma shiryatar da mu zuwa ga sunnonin fidira, da suka hada da: yanke farce, gusar da gashin hamata da na mara; Kaman yanda ya zo a Hadisi Sayyida A'isha (Allah ya kara yarda da ita) ta ce: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Abubuwa goma suna cikin fidira: aske gashin baki, da rage gashing emu, da asuwaki, da shaka ruwa, da yanke farce, da wanke wuraren da dauda yake taruwa, da tsige gashin hamata, da aske gashin mara, da yin tsarki da ruwa) maruwaicin ya ce: na manta na goma, ina ganin kaman (Kurkurar baki ne) [Muslim].

Share this:

Related Fatwas