Kwadaitarwa da shari'a ta yi wajen ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kwadaitarwa da shari'a ta yi wajen tsaftace hanyoyi

Tambaya

Ta yaya shari'a ta kwadaitar game da tsaftace hanyoyi?

Amsa

Shari'ar Musulunci ta kwadaitar game da tsaftace hanyoyi, ta hana yin fitsari a hanya, da ma duk abin da za a iya hade shi da haka na jefa najasa, ko abubuwan kazanta; an ruwaito Hadisi daga Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi), cewa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ku kiya yi la'anannu biyu) suka ce: mene ne la'anannu biyu ya Manzon Allah? Sai ya ce: (Wanda yake bayan gida a hanyar mutane, ko a inuwar da suke hutawa) [Muslim].

Ya kuma kwadaitar akan kawar da kazanta ga barin hanyoyi, ya sanya hakan a matsayin kaso ne daga cikin kashe- kashen imani, (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Imani kaso saba'in da wani abu –ko sittin da wani abu ne-, wanda ya fi shi ne faxin "La'ilaha illalLahu", mafi kankantarsa kuma shi kawar da kazanta ga barin hanya, kunya ma kaso ne daga cikin imani) [Muslim].

 

Share this:

Related Fatwas