Manhaji na fahimta da sasinsa a wur...

Egypt's Dar Al-Ifta

Manhaji na fahimta da sasinsa a wurin masu tsattsauran ra’ayi

Tambaya

Mene ne ginshikin ilimin da masu tsattsauran ra’ayi su ke samun iliminsu?

Amsa

Masu kafirta mutane suna fama da rashin ingantaccen gini na fahimta da kuma abubuwan da suke na farko farko da aka cimma matsaya akan hakan a cikin tsarin karatu da karantarwa da fatawa da kira zuwa ga Allah, shine abin da ake kira da “juyayyen tunani”  to wannan shine yake haifar da kuskure a farkon lamari da kuma karshensa, a bisa wannan la’akarinne muke iya gane cewa akwai burbushin wannan tunanin a kwakwalen kungiyoyin ‘yan ta’adda, wannan ya bayyana ne ta hanyar fahimtarsu ga nassosin shari’a, sai muga suna ta canza ma’anonin abubuwa masu yawa na rayuwarmu ta yau da kullum, ta inda suke canza abu mai kyau zuwa mummuna, yayin da kuma abu mai muni ke canzawa zuwa mai kyau, irin wannan shi ake kira da “juyayyen tunani” tsarin dalan gini shine a fara gini a fadade ayi ta tafiya har a kai zuwa kololuwa kamar dai yanda ake iya ganin hakan a dalan gini na gyada ko wani abu mai kama da haka, to tsarin juyayyen tunanin a sashen manhajin da ake gina hukunce hukunce na shari’ar musulunci akansa kuskure ne bisa la’akari da wasu abubuwa ta bangarori da dama, shin na fannin ilimi ne ko ko manhaji ko halayya ta shari’a.

Tsarin manhajin da aka gida ilimin musulunci akansa yana dogara ne bisa ababuwa masu matukar muhimmanci, saboda dukkan wani tsari mafi dacewa ga kowani abu shine a gina shi bisa daidaito ba wai a jirkice ba, domin hakan ne ke sanyamu mu fara daga abu mai mafi muhimmanci sannan mai muhimmanci, sabanin abinda muke iya gani daga kungiyoyin ‘yan ta’adda a cikin tsarin ilimi na shari’a, domin su na da tsare tsare da suka sabawa Ahlus sunna a wurin da’awa. Da neman ilimi da kuma karantarwa da fatawa.

Share this:

Related Fatwas