Ma’anar dagutu a wurin kungiyoyi ma...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar dagutu a wurin kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi

Tambaya

Ta yaya kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi suka sauya ma’anar dagutu?

Amsa

Hakika masu tsattsauran ra’ayi sun sauya ma’anar kalmar “Dagutu” daga manufar kalmar zuwa wani abu daban, wato dai sun dangantakanta ma’anar kalmar da shugabanni da kuma sauran al’ummu, saboda shugabanni suna yin hukunci da abin da ba Allah ne ya saukar ba -a bisa mummunar zatonsu– wai al’ummu sun aminta da hakan ba tare da nuna bijirewa ba, amma a zahirin gaskiya ko dokokin kasar Misra daga hukunce hukuncen shari’ar Musulunci aka tsamo su, kamar dai yanda sashe na biyu na kundin tsarin mulkin kasar Misra ya bayyana cewa hukunce hukuncen shari’ar Musulunci su ne madogaran shari’ar na asali, kuma Musulunci shi ne Addinin kasar ta Misra, sannan harshen Larabci shi ne harshen hukuma, hakika kalmar “Dagutu” ta zo cikin Al’kur’ani Mai girma a wurare da daman gaske, daga ciki akwai inda Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake cewa: (Shin ba ka ga wadanda suke raya cewa wai sun yi Imani da abin da aka saukar gareka, da ma wanda aka saukar kafin kai suna son su kai wa dagutai shari’oinsu domin su yi mu su hukunci ba) [An- Nisa’i: 60], kalmar “Dagutu” anan tana iya daukar fuskoki da daman gaske, domin akan iya tsinkayar da ita ga mutum daya tilo, ko kuma jam’i, ko namiji ko kuma mace. Imam Al’maturidi ya ce: Kalmar “Dagutu” tana nufin duk wanda ake bautawa wanda ba Allah ba, domin wannan ayar ta sauka ne akan wasu munufukai da suka kasance suna kai wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) wani sashe na hukunce hukunce su, bayan da ya yanke musu hukunci sai suka ki amincewa da hukuncinsa domin ya sabawa son zuciyarsu.

Share this:

Related Fatwas