Tsananta yawan kudin sadaki da mats...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsananta yawan kudin sadaki da matsalolin da ke tattare da shi

Tambaya

Mene ne hukuncin shari’a akan tsananta kudin sadakin aure da tasirin haka?

Amsa

Shi dai tsananta sadaki ba ya cikin sunnar Musulunci, saboda manufa ta asali na yin aure shi ne kamewar saurayi da budurwa daga yin alfasha, Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam): (Mafi girman mata wurin albarka sune wadanda sadakinsu ya yi sauki) Al-Hakeem a cikin “Al-Mustadrik”.

Abin da ya kamata shi ne rashin tsananta sadaki, mahaifi ya kamata ya saukaka auren yayansa ta dukkan hanyoyi idan har manemin auren mutum ne nagari, wanda hakan ne zai kare samarinmu da ‘yan matanmu daga kauce hanya, hakika Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya gabatar mana da nasiha mai girma inda ya ce: (Idan wanda ya zo neman auren yarku da kuka aminta da addininsa da dabi’unsa to ku aurar masa, idan baku aikata haka ba to zai kasance fitina da barna mai yawa a doron kasa) Tirmizi.

Share this:

Related Fatwas