Tsayawa a kan kabari bayan an birne...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsayawa a kan kabari bayan an birne mamaci

Tambaya

Menene hukuncin tsayawa akan kabari bayan rufe mamaci domin yi masa addu’a da nema masa gafara?

Amsa

Tsayawa akan kabari bayan an rufe mamaci domin nema masa gafara da yi masa addu’a yana daga cikin sunnoni da ake bi, an karbo daga  Amirul muminina Usman zul- Nuraini Allah ya kara masa yarda ya ce: Annabi S.A.W. ya kasance idan ya kamala rufe mamaci yakan tsaya akan kabarinsa ya ce: (Ku nemawa dan’uwanku gafara, sannan ku yi masa addu’an samun sabati wurin tambaya, domin shi a yanzu ana tambayarsa). {Dauda ne ya ruwaito hadisin}.

Imam Al’Nawawi yana cewa a cikin “Al’azkar” (1\161) : {Akan so a zauna a wurinsa kamar awa daya, gwargwadon yanda za a soke rakumi a raba naman, sannan masu zaman su zauna domin yin karatun Al’kur’ani, da yiwa mamaci addu’a, yiwa mahalarta wurin wa’azi, tare da ba su labaran mutane nagari, da halayen salihai, Imam Shafi’a da sahabbansa sun ce : Akan so da su karanta wasu ayoyi na Al’kur’ani a wurin mamaci, sai suka ce: Idan sun sauke Al’kur’ani to da hakan yafi}. I H.

Share this:

Related Fatwas