Tsayawa akan kabari bayan rufe mama...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsayawa akan kabari bayan rufe mamaci.

Tambaya

Mene ne hukuncin tsayawa akan kabarin mamaci bayan rufeshi domin yi masa addu’a da kuma nema masa gafara?

Amsa

Shi dai tsayawa akan kabari bayan rufe mamaci domin neman masa gafara da yi masa addu’a yana daga cikin sunnonin da ake bi, an karbo daga Amirul Muminina Usman dan Affan – Allah ya kara masa yarda – ya ce: Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya kasance idan ya gama rufe mamaci yakan tsaya a wurin kabarin ya ce: (Ku nemawa dan’uwanku gafara ku roka masa tabbata, domin shi a yanzu ana tambayarsa) Abu Dauda.

Imam An-Nawawy yana cewa a cikin littafin “Al-Azkar” (1/161): ( Anso a zauna a wurin mamaci bayan rufe shi na sa’a guda, gwargwadon yanda za a tsire rakumi a raba namansa sai wanda suke wurin su shagalta da karanta Alkur’ani, da yi wa mamaci addu’a, da yin wa’azi, tare da bayar da labaran mutanen kirki, da halayen salihai, Imam Shafi’i da sahabbansa sunce:Akan so a karanta wani abu na ayoyin Alkur’ani a wurin mamaci, sai sahabbansa suka ce: Idan sun sauke Alkur’anin dukansa to yafi).

Share this:

Related Fatwas