Gudummuwar da Sufanci yake bayarwa ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Gudummuwar da Sufanci yake bayarwa wajen gina Musulmai mai daidaito

Tambaya

Wace Gudummuwa ce Sufanci yake bayarwa wajen gina Musulmai mai daidaito?

Amsa

Sufanci shi ne muƙamin al- Ihsan da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi sharhinsa da cewa: (Ka bauta wa Allah kaman kana ganinsa; domin idan kai ba ka ganinsa, to kuwa shi tabbas yana ganinka) [al- Bukhari da Muslim], lallai malamai sun yi ta kawo ma’anoni na wannan ilimi, abin da har ya ƙetare ma’anoni ɗari biyu, amma duk da haka idan muka dubi dukan ma’anonin za mu iya cewa sun haɗu ne akan ma’anoni guda biyu; na farko: Yaƙar zukata daidai da yadda Shari’ar Musulunci ta tabbatar, inda ta wannan yanayin ne ake samun yanayi maɗaukaki, da tsarkin ruhi, na biyu: Mushahadar haƙiƙa, abin da ake kira da haƙiƙa a wurin Sufaye  shi ne:  La’ilaha illalLah, a cikin kyawawan maganganunsu akan haka akwai: gwargwadon ƙoƙarinka, gwargwadon mushahadarka, da Sufanci ɗabi’u ne kyawawa, duk wanda ya fi ka a fagen ɗabi’u kyawawa, to ya ɗara ka a cikin Sufanci, a cikin sharuɗɗan Sufanci akwai samar da shaihi mai tarbiyya da shi ne zai jagoranci yi wa muridai tarbiyya, ya shiryatar da su zuwa ga hanyar Allah, saboda Allah mai girma da ɗaukaka, a cikin abubuwan da suke bayyana fifikon Sufanci akwai kasancewarsa ilimi da Isnadinsa ya dangana da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), kuma wannan it ace hanyar da idan har Musulmi ya bi ta, to kuwa ya katange kansa daga faɗawa cikin munanan ɗabi’u, irin su girman kai, da yi wa bayin Allah mummunan zato, da shiga cikin abin da babu ruwansa, da kuma rungumar duniya.

Share this:

Related Fatwas