Ta'assubanci da wuce gona da iri a ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ta'assubanci da wuce gona da iri a addini

Tambaya

Ta yaya shari'a ta yi gargadi game da ta'assubanci, da wuce gona da iri a addini?

Amsa

Shari'ar Musulunci ta hana guluwwi da ta'assubanci da wuce gona da iri a cikin al'amarin addini; abubuwan da suke kai wa zuwa ga yada kiyayya mai muni a tsakanin mutane, suke kuma yin tasiri mai muni a zaman lafiyarsu da rayuwar zamantakewa, su kuma kawo tabarbarewar tsaro da kwanciyar hankali a cikin kasashe, a hanyar Musulunci wajen kira zuwa ga Allah ama dogaro akan kyautatawa mutane, da rashin cin mutuncin wanda ake da sabani da shi a mazhaba ko imani da addini, Allah mai girma yana cewa: (Kay i kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau, ka yi jayayya da su da abin da ya fi zama mai kyau, lallai Ubangijinka shi ne ya san wanda ya bace ga barin hanyarsa, shi ne kuma wanda ya fi sanin shiryayyu) [an- Nahl: 125].

 

Share this:

Related Fatwas