Tafiya zuwa garuruwan da ba na Musu...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tafiya zuwa garuruwan da ba na Musulmai ba.

Tambaya

Mene ne hukuncin tafiya zuwa garuruwan da ba na Musulmai ba da zama a cikinsu? 

Amsa

Lallai tafiya zuwa garuruwan da mafi yawan mutanen garin ba Musulmai bane, to a wannan babu wani haramci a shari’ance, matukar dalilin tafiyarsa zuwa kasar yana daga cikin al’amura da shari’a ta halasta, kamar tafiya domin neman ilimi ko kuma aiki ko kasuwanci da neman halaliya ko kuma shakatawa, tare da cewa shi Musulmi matafiyi ya  kiyaye addininsa ta yanda ba za a fitinesa kan addininsa ba, ko ransa ko mutumcinsa, ya kuma tabbatar ba za a tilasta masa ya bar addininsa ba, ko kuma aikata haramtattun abubuwa kamar shan giya ko aikata alfasha kamar zina ko sata da sauran abubuwan da Allah mai girma da buwaya ya hana, kuma ya zama yana da ikon gudanar da addininsa cikin ‘yanci da walwala ba tare da wani tarnaki ba, to fa wadannan su ne wajiban shari’a da babu sabani a cikinsu kamar dai tsayar da salloli na farilla, idan haka ya tabbata to zaman Musulmai a cikin garuruwan da ba na Musulmai ba halas ne, dalilin haka shi ne izinin da Annabi SallallaHu AlaiHi Wasallam ya yiwa baffansa Abbas bin Abdulmuddalib Allah ya kara masa yarda na ya gudanar da rayuwarsa a garin Makkah kafin a bude garin da Musulunci, dalilin haka kuwa shi ne don kiyaye kansa da rashin tsoron fitina a addininsa, idan har wadannan abubuwan da aka ambata suka koru ga Musulmai to tafiya irin wadannan garuruwa ya haramta garesu.

Share this:

Related Fatwas