Kira zuwa ga Allah a musulunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Kira zuwa ga Allah a musulunci

Tambaya

Wace hanya ce ingantacciya ta shari’a wurin bijirar da musulunci ga mutane? Shin ta hanyar jihadi ne ko ta yaya?

Amsa

Hakika malaman shari’a sun bayyana cewa a duk sanda musulmai suka gabatar da farali na kifaya na tsare iyakokin kasashen musulmai, to kira zuwa ga Allah ya wadatar da yin jihadi ta hanyar yakar kasashen da ba na musulmai ba, ai yanda lamarin yake ma shine a duk sanda kira zuwa ga Allah ya zama mai amfani a wuri to babu bukatar karkata zuwa ga jihadi, ba wai kashe wadanda ba musulmai bane abin lura, shi jihadi wata hanya ce ba wai tana nufin  tsantsagwaron kisa bane, sai suka ce : “ Shi wajibcin jihadi shine wajibci na hanyoyin samuwarsa ba wai manufar aiwatar da shi bane, saboda abin nufi da yaki shine shiryatarwa da abinda ke bayan haka na shahada, amma kashe kafirai ba shine abin nufi ba koda kuwa shiriya ya wanzu wurin tsayar da dalili ba tare da jihadi ba to shine mafi dacewa daga yin jihadin”.

Tushen kiran wani zuwa ga addinin Allah da kuma yin mu’amala dashi shine tausayi da rangwame gareshi, domin fadin Allah Ta’ala inda yake Magana da Annabinsa  SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam : (Ba mu aika k aba face sai don ka kasance rahama ga talikai) {Anbiya: 107} Lallai wannan bayanin na Al’kur’ani tare da fadadar ma’anarsa wanda ya kunshi dukkan bigere, to bai takaita da wani wuri ya bar wani wuri ba, ko kuma lokaci tare da canzawarsa, da al’ummu masu shudewa, don haka bai shafi wani lokaci yabar wani ba, dukkan wadannan halayen – Na zaman lafiya ko yaki – to ba su takaita da wani yanayi sun bar wani ba, mutane baki dayansu, muminansu da kafiransu Larabawansu da Ajamawansu, hakanan bai kebance wasu yabar wasu ba, wanda hakan shi ke sanya mutum cikin nazari da lura da girman annabtan shugaban mutanen farko da na karshe kamar yanda Al’kur’ani ya bayyana : (Ba mu aike ka ba sai don ka kasance rahama ga talikai) {Anbiya 107}ai rahama ce gamammiya wacce sasanninta suka bayyana a kowani bangare na Annabi SallaHu AlaiHi wa aliHi wasallam a bisa wannan duniyar da kuma mutanen da ke tare da shi.

Share this:

Related Fatwas