Karkasuwan duniya a fikihun musulunci
Tambaya
Mene ne matsayar malaman fikihu kan rarraba kasashen duniya fiye da daya?
Amsa
Jumhorin malaman fikihu sun karkasa kasashen duniya zuwa gidan musulunci da gidan yaki, da kuma gidan alkwari da yarjejeniya da sulhu, don haka duk da wannan kasha kashen ana kiransa da suna : gidan yarjejeniyar zaman lafiya, Hanafawa na ganin cewa kasashen duniya sun kasu zuwa gidan musulunci da kuma gidan yaki, wasu kuma cikin malaman fikihu na daban sun kasa kasashen duniya zuwa : “gidan aminci” da “gidan yaki” da “gidan sulhu” da “gidan alkawari” da “gidan alkawari” da kuma “gidan aminci” inda suka tabbatar da cewa : matukar kasa – kowace kasa – ana tsayar da sallah a cikinta kamar yanda aka saba, sannan an baiwa kowa damar yin bautarsa – kowa kuwa na a kasashen musulmai bane – to abisa wannan ana kallon wannan kasa a matsayin kasar zaman lafiya da aminci, ba gidan yaki bane, hakanan sun tabbatar da cewa duk wata kasa dake karkashin dokokin Majalisar Dinkin Duniya to tana karkashin “Gidan alkawari” ne, ba gidan yaki ba, mafi yawan kasashen duniya a wannan lokacin suna cikin kasashen sulhu da zaman lafiya ne a zahiri, wannan kuwa ya kasance ne sakamakon tarayyar da kasashen musulmai sukayi da wasunsu cikin al’ummu kan alwarurruka da yarjejeniyoyin kasa da kasa, a bisa wannan la’akarin dukkan kasashen duniya suka kasance kasahen aminci, ba kasashen musulunci ba, saboda kasar musulunci ita ce wacce musulmai ke jagorantarta.