Ma’anar kiyaye jini a Musulunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar kiyaye jini a Musulunci

Tambaya

Mene ne ma’anar kiyaye jini a Musulunci, wasu abubuwa ne suka wajabta bayar da wannan kariyar?

Amsa

Alfarmar jini a Musulunci yana nufi bai wa jinin kariya daidai da yanda shari’a da dokoki da al’ada suka shimfida, hakan yana cikin manyan manufofin Shari’ar Musulunci, ba a halatta keta alfarmar jini da sunan shari’a, hasali ma duk wanda ya aikata haka yana da mafi tsananin hukunci a duniya da lahira, saboda hakan yana cikin manyan laifuffuka, Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Manyan laifuffuka su ne: hada Allah da wani, da kashe ran dan Adam) [al- Bukhari da Muslim], ita shari’a ita ce take bai wa jini kariya da alfarma, saboda Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Kada ku kashe ran da Allah ya haramta a kashe shi, sai da hakki, wannan ne abin da Allah ya yi maku wasiyya, ko za ku hankalta) [al- An’ami: 151].

Lallai Musulunci ya zo ne saboda ya kiyaye hakkoki, ya kuma yada tsaro da aminci da zaman lafiya, ya kuma bai wa jini da dukiya da mutunci kariya, na kada a keta su sai da hakki, saboda haka duk wanda ya dauki jini ba a bakin komai ba, shin jinin na Musulmai ne, ko na wadanda ba Musulmai ba, to kuwa yana aiki ne akan saba wa shari’ar Musulunci.

Share this:

Related Fatwas