Yanda mutanen turai suke kallon Mus...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yanda mutanen turai suke kallon Musulunci

Tambaya

Wane tasiri kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ‘yan ta’adda suke yi akan surar Musulunci a duniya?

Amsa

Lallai aiki wajen gyara surar Musulunci abu ne da shari’a kanta ta nema; ganin cewa akwal nassoshin shari’a masu yawa da suka bukaci haka, ta hanyoyi na zahiri da ba za su kai zuwa ga bacin asali ba, ya kamata duk wata dangantaka tsakanin kasashe ta kasance akan ingantacciyar turba ba tare da tsoro ko razani ba, da haka dole surar ta zama nagartacciya, wannan shi ne abin da nassoshi suke nuni zuwa gare shi. sai dai su masu tsattsauran ra’ayi bas a fadaka da haka a mafi yawan lokuta, suna saba wa koyarwar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) game da wannan al’amari, babu abin da yake fito da wannan sabawar fili kaman irin yanda suke aike wa da mayakansu su yi shigar burtu cikin ‘yan gudun hijira da wasu kasashe suka amince da su ba su mafaka zuwa wani lokaci, kamata ya yi a ce wadannan mutane sun bayar da sanarwar cewa ba za su taba kai wa wadannan kasashe hari ba, ko kuma a aikace su kame ga barin kai masu hari, ko da kuma ba su sanar da hakan ba, a babin saka alhairi da alhairi; domin sun bai wa ‘yan uwansu mafaka, idan har suna kallonsu a matsayin ‘yan uwa a gare su, su yi koyi da shiryatarwar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) lokacin da ya yi mu’amala da jama’an matar da suka nemi ta ba su ruwa su sha, kaman yanda ya zo a cikin sahihul Bukhari, inda ya ce: (Musulmai tun daga wannan lokaci ba su kai masu hari idan sun kai hari akan mushrikan da suke gefensu, ba kuma sa aukawa gidajensu, sai wata rana ta ce wa mutanenta: Ni fa ina ganin mutanen nan ba kawai suke barinku ba, ashe bai kamata a ce kun shiga Musulunci ba? sai kuwa suka yi mata biyayya, suke shiga Musulunci.

Share this:

Related Fatwas