Yin amfani da maganin da yake kunshe da sinadarin "Gelatin"
Tambaya
Mene ne hukuncin yin amfani da maganin da yake kunshe da sinadarin "Gelatin"?
Amsa
Idan shi wannan sinadarin na "Galatin" a ciro shi ne daga dabbar da ake ci, kuma an yankata, to shari'a ba ta hana yin amfanin da irin wannan maganin ba, amma idan dabbar ba wadda ake ci ba ne, ko kuma ba a yanka ba, to anan za a duba: idan sinadarin ya sauya daga dabi'arsa, ya zama sauran sinadaren maganin sun rinjaya, ta yanda ba za a iya kiran abin da sunan sinadarin ba, to a nan shari'a ba za ta hana amfani da shi ba, sai dai dole ne a koma zuwa ga likita a ji ta bakinsa game da amfani da irin wannan magani.